Jagororin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, sun ce ba za su amince da kai masu ziyarar manyan jami'an diplomasiyya ba, saboda masu ziyarar zasu iya fuskantar babban hadari.
A yau ne ya kamata wakilai daga kungiyar Ecowas da kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya su garzaya zuwa kasar a kokarin da ake na lalubo bakin zaren sasantawa.
Sai dai shugabannin juyin mulkin sun fadawa Ecowas cewa takunkumi da barazanar mamaye kasa da kungiyar tas saka, sun haifar da fushi daga bangaren jama'a, a saboda haka ba za a iya karbar bakuncin tawagar jami’an a halin yanzu ba.
Rahotanni daga Yamai babban birnin kasar sun ce mutane da dama sun yi maraba da juyin mulkin a matsayin shakar iskar yanzi , duk da cewa an zabi hambarraren shugaban kasar Mohamed Bazoum ta hanyar dimokradiyya.