On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jagororin Jam'iyyun APC Da NNPP A Jihar Kano Na Jifan Juna Da Laifin Bangar Siyasa

Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bukaci Jami'an tsaro su dauki mataki akan dan takarar gwamna a karkashin Jam'iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge shi da mayar da gidansu na gado dake mazabar Chiranchi a karamar hukumar Gwale a matsayin ofishin yakin neman zabe da tara 'yan daba da makamai da kuma gudanar da hada-hadar kwayoyi.

Shugaban Jam'iyyar ta APC, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a nan Kano, ya na mai  cewa ko a ranar alhamis din nan sai da aka halaka wani matashi a wurin, yana mai cewa idan rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano, ta gaza daukar mataki a kansa, zasu mika bukatar hakan ga Babban sifeton'yan sanda ko su shigar da kara kotu. 

A nasa martanin mai magana da yawun Dan takarar Jam'iyyar  NNPP, Engineer Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, yace jawabin na Abdullahi Abbas, kokari ne na kawar da hankulan Jami'an tsaro kada su damke shi sakamakon ire-iren kalaman tada hankali da yake yi, yana mai cewa kamata yayi ya kai kansa gaban Jami'an tsaro domin bincikarsa akan kalaman da yake yi.

Dawakin Tofa, ya kara da cewa a shirye suke idan bukatar hakan ta taso,  Jami'an tsaro su duba ofishin nasu idan an sami makami ko kwaya  a hukunta su dai-dai da doka. Daga nan sai ya bayyana cewa Jam'iyyar NNPP na da  damar bude office a duk inda take bukata.