On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Jagoran 'Yan Fashin Daji Bello Turji Ya Bada Umarnin Tsare Masu Kai Harajin Kariya A Jihar Zamfara

Rahotanni na nuni da cewa, fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya tsare wasu mazauna garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, su biyar.

Bayanai sunce an tsare mutanen ne bayan sun kai Naira miliyan 10 da dubu dari 5 amatsayin harajin kariya da ya kakabawa al’ummar garin.

Makonni biyu da suka gabata, Turji ya sanya Naira miliyan 20 amatsayin haraji ga mutanen Moriki da ke da nisan kilomita 33 a kan hanyar Kaura Namoda  zuwa Shinkafi.

Al’ummar garin sun samu damar tara Naira miliyan 10.6 sannan sukayi amfani da Naira dubu 100 wajen sayen  taba sigari da burodi sa sauran kayyaki kamar yadda ‘yan fashin dajin  suka umarce su.

An wakilta mutanen yankin su bakwai su je kai kudin, sai dai bayan da tawagar masu kai kayan suka isa wurin, yaran Turji goma sha bakwai suka hau doki zuwa wurin suka nemi a basu kudin da sauran kayayyaki, inda  ran Turji ya bachi akan cewa kudin da aka kawo Naira miliyan 10 da dubu dari 5 ne ba Naira miliyan 20 da ya bukata ba.

Nan take Turji ya umarci yaransa  da su tsare mutum biyar daga cikin bakwai na tawagar masu kai kayan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce zai yi bincike kan  hakikanin abin da ya faru.