Kungiyar iyayen yara ta kasa ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da hana ma’aikatar ilimi ta kasa yin karin kudin makaranta da kaso 100 bisa 100, da Daliban kwalejojin gwamnati da kuma na Makarantun Hadaka ke biya a kasar nan.
Kungiyar ta baiyana karin a matsayin kuntatawa, sannan kuma bai dace da lokacin da ake ciki ba, wanda kuma ya ci karo da alkawarin da shugaban kasa Tinubu ya yi,na kyautata rayuwar iyayen yara, sakamakon kalubalen cire tallafin mai.
A wata sanarwa da babban jami’in kungiyar na kasa, Monday Eze ya fitar, Ya koka kan karancin gogaggun malamai da dakunan kwana da Ajujuwa da kuma rashin bada horo kan darussan kimiyya da fasaha a kwalejojin kimiyya da fasaha guda shida da ake dasu a shiyyoyin kasar nan.
Ya bukaci sabuwar gwamnati data samar da muhimman kayayyakin a makarantun domin ingantasu.