On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Injiniyoyi Mata A Najeriya Sun Roki Shugaba Tinubu Ya Sahale Su Gyara Matatun Man Kasae Cikin Shekara 'Daya

Kungiyar kwararrun Injiniyoyi mata ta Najeriya APWEN tayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya baiwa injiniyoyi mata damar gyara matatun mai na kasa.

Shugabar kungiyar, Atinuke Owolabi ce ta yi wannan kiran yayin taron lacca da taron shekara-shekara na kungiyar a Legas.

Owolabi ta ce injiniyoyi mata a Najeriya za su iya farfado da matatun mai gaba daya a cikin shekara 1 kacal.

Ta ce Najeriya na bukatar rage dogaro ga kwararrun kasashen waje tare da bada damammaki ga injiniyoyin cikin gida wadanda suke da  kwarewa  daidai ko suka wuce na kasashen wajen..