Bayanan da suka fito daga cikin kudurin daftarin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana, da majalisar zartarwa ta kasa ta amince da shi a jiya, ya nuna cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta zata samu naira milyan dubu 18 domin gudanar zaben gwamnonin jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Atiku Bagudu, wanda ya zanta da manema Labarai na fadar shugaban kasa, kan abunda taron ya kunsa.
A wani bangaren kuma, Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fitar da bayanan yawan katinan zabe na din-din da aka karba da kuma wadanda ba’a karba ba a jihohin guda ukku.
Hukumar ta roki masu ruwa da tsaki da su kwana da sanin cewar duk inda aka samu kuri’ar da aka dangwala a rumfar zabe ta haura adadin katin zaben da aka karba a rumfar zaben, to zai kasance an samu aringinzon kuri’a.