On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

INEC Na Shirin Aikewa Da Na'urar BVAS Fiye Da Dubu 11 Domin Zaben Gwamna A Jahohin Bayelsa Da Imo Da Kuma Kogi

Hukumar zabe ta kasa INEC  za ta tura na’urorin tantance masu kada kuri’a guda dubu 11 da 355 domin tantance masu kada kuri’a a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma Imo.

Wani babban jami’i a hukumar da aka sakaya sunansa ya bayyana haka ga wakilinmu a karshen mako.

A cewar INEC, jihar Bayelsa na da rumfunan zabe dubu 2 da 244 yayinda   Kogi ke da rumfunan zabe dubu 3 da 508 sai Imo mai rumfunan zabe dubu 4 da 758.

Idan dai za a iya tunawa, zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, sun gamu da  matsalar Na’urar  BVAS.