Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta, tace tana kan aikin wallafa cikakkun bayanaan yawan ‘yan Najeriyar da suka yi rijistar katin zabe, gabanin babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
Shugaban hukumar, farfesa Mahmood Yakubu ne ya baiyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, domin yin nazari kan kundin dokoki da tsare-tsaren kada kuri’a ga ‘yan gudun hijira da aka yiwa gyaran fuska, yau a Abuja.
Yace sunayen, zai kunshi sabbin wadanda suka yi rijistar katin zabe, kari akan milyan 84 da ake dasu.
Bugu da kari, Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, yaga baiken wasu kungiyoyin farar hula dake baiyana cewa, Hukumar zaben ta kasa bata da niyyar baje kolin wadanda suka yi rijistar katin zabe, inda hukumar ta baiyana cewa tayi baje kolin rijistar katin zaben har sau ukku, wand aya hada da ranar 24 da 30 ga watan Satumbar 2021, da kuma 24 ga watan Disambar 2021.