On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ina Da Kwarewar Da Ake Bukata Wajen Mulkin Kano - Gawuna

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana cewa yana da gogewar da ake bukata ta shugabanci da gudanar da mulkin jihar Kano har zuwa wani matsayi mafi girma.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Hassan Musa Fagge, babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, ta bayyana hakan ne yayin wani shiri da gidan talabijin na kasa NTA  ya gabatar a jiya.

Ya bayyana cewa samun damar yi wa jihar Kano hidima a matsayin shugaban karamar hukuma sau biyu, sannan  ya rike kwamishinan noma sau uku da kuma mataimakin gwamnan jihar Kano hakan ya  ba shi fifiko a kan sauran masu neman kujerar gwamnan.

Ya kuma kara da cewa hadin kan da ake samu a jam’iyyar zai taimaka matuka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.