Cibiyar dake kula da kanana makamai ta nuna damuwar ta kan yarda ake samun karuwar cibiyoyin tsaro masu zaman kansu dake bayyana kawunan su amatsayin wadanda gamnati ta sahalewa kula amfani da makamai a kasarnan, musamman ma a yankin Arewa ta tsakiya.
Jami’in tuntuba na yankin Major Janaral Hamza Bature mai ritaya ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manma labarai a shalkwatar cibiyar dake Minna.
Yace bayanan da cibiyar ta gano a kwanan nan sun bayyana cewa irin wadannan kungiyoyi sun kai ga yaudarar al’umma jihar Kogi da yi musu alkawarin basu ayyukan yi don taimakawa wajen kwace kananan makamai.
Bature ya koka kan cewa ayyukan irin wadannan kungiyoyi da basu da sahalewar gwamnati, suna kawo tsaiko ga ayyukan cibiyar na tabbatar da ganin Najeriya ta kasance kasar da ba’a yin amfani da kananan makamai barkatai, yayin da kuma yace hakan zai iya bata sunan cibiyar.