A daidai lokacin da ake fama da karancin kudi, babban bankin Najeriya ya sha alwashin hukunta duk wani banki da masu sana'ar POS da suka kawo cikas ga zagayawar takardun Naira a hannun Jama'a.
Gwamnatin tarayya ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan karancin takardun kudi da ake fuskanta, inda ta ce za a samu sauki a shekara mai zuwa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ya ce ba da gangan aka samu matsalar ba.
Idris wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta samu, ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a samu karin kudade a kasuwanni idan an shiga sabuwar shekara.
Ya ce babban bankin Najeriya na yin duk mai yiwuwa don ganin an shawo kan al'amarin, ciki har da samar da sabbin takardun kudi na Naira.
Shima a wata sanarwa ranar Alhamis da bankin ya wallafa a shafin Twitter, CBN ya fusata kan masu boye kudaden l, kuma ana gudanar da bincike kan al’amuran da aka ruwaito da ka iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasa.
Don haka CBN ya gargadi bankuna da masu PoS da su Kaucewa fuskantar takunkumi.