Yayin da ya rage kwanaki goma sha shida a fara gudanar da babban zaben kasar nan, akwai wasu rahotanni dake baiyana cewa karancin sabbin kudin da aka sauyawa fasali ka iya kawo tazagaro wajen gudanar da zaben mai zuwa.
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya baiyana haka a yayin ganawarsa da gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele a shalkwatar bankin dake Abuja a ranar Talata.
Ya kara da cewa mafi yawa daga cikin wadanda zasu gudanarwa da hukumar wasu aikace aikace a lokacin zaben basu da asusun banki.
A saboda haka shugaban hukumar zaben ta kasa,Ya yi kira ga Babban bankin kasa da ya gaggauta magance matsalar da shirin takaita zagayawar kudi a hannun jama’a ta haifar a fadin kasa a yanzu haka.