A yayin da ya rage kasa da kwanaki 100 a gudanar da babban zaben kasar nan mai zuwa, Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta ce zata buga takardun kada kuri’a milyan 187.
Kwamishinan hukumar na kasa, kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe Festus Okoye ne ya baiyana haka, a yayin wani zauren tattaunawa da shugabannin Editoci na kasa a Abuja.
Yace za’a yi amfani da takardun dangwala kuri’a milyan 93 da dubu 500 a zaben shugaban kasa da za’a a yi ranar 25 ga watan Fabarairun shekara mai zuwa, sai kuma ragowar takardun kada kuri’a milyan 93 da rabi da za’a yi amfani a zaben cike gurbi na shugaban kasar idan har ta kaiga an samu haka.