Hukumar Zabe Ta kasa Mai zaman Kanta INEC, Ta sake fadakar da Yan Najeriya cewa , Hukumar zata dakatar da aikin rijistar katin zabe na din-din da ake kan yin a da kwanaki Tara masu zuwa .
Wani jami’in hukumar, Luka Buba ne ya baiyana haka, kazalika shima babban jami’in kula da rijistar katin zabe na Hukumar, Temi, Ya baiyana cewa Hukumar zata soke duk wata rijistar katin zabe data samu anyi ta har sau biyu.
Kazalika yace za’a iya magance matsalolin da suka danganci bacewar katin zabe akan shafin hukumar zabe na Internet.
A wani bangaren kuma,Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, Tace a yaune zata wallafa sunayen yan takarar da jam’iyyu suka gabatar mata, a matsayin yan takararsu na gwamna da Yan Majalisun Dokokin Jihohi na fadin kasar nan.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya baiyana haka a lokacin da yake rantsar da sabon kwamishinan zabe na birnin taraiyya Abuja.
Sai dai kuma, Shugaban Hukumar ya baiyana damuwarsa game da karuwar rikicin cikin gida a tsakanin jam’iyyu, wanda shine ya zama babban tarnaki ga tsarin gudanar da zabe a kasar nan.
Ya kara da cewa, hukumar zata cigaba da hada kai da jam’iyyu domin wayar masu da kai dan ganin sun kasance masu bin doka da oda.