Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta ta zargi wasu ‘yan siyasa da siyan katinan zabe na din-dindin domin yin amfani da lambobinsu gabanin babban zabe na shekarar 2023.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan hukumar mai kula da birnin tarayya Abuja da jihohin Nasarawa da kaduna da kuma Filato mohammed Haruna.
Ya ce kwanan nan an yanke wa wasu mutane biyu hukunci, bisa laifin mallakar katinan zabe ba bisa ka’ida ba a jihohin sokoto da kano.
Kalaman da hukumar ta INEC tayi, ya janyo cece-ku-ce daga wasu masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada da Kungiyar afenifere, data Pandef sai kungiyar ohanaeze ndigbo da sauransu.