Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta caccaki fitaccen mawakinan , Davido, wanda ya kasance ‘Da ga Dan uwan zababben gwamnan jihar Osun, Sanata, Ademola Adeleke, kan wa’adin da ya bawa hukumar zabe, akan ta tabbatar ta bawa kawunsa Adeleke takardar shaidar lashe zabe.
Sanata Adeleke na jam’iyyar PDP ya doke gwamna mai ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC wadda ke yin mulki a jihar.
Idan ba’a manta ba, Mawaki Davido ya tuhumi Hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta, akan dalilan da yasa ta ki mikawa kawun nasa, takardar shaidar lashe zabe bayan sa’o’i 48 kamar yadda doka ta tanada.
Da yake mayar da martani ta cikin wata sanarwa da hukumar a zaben ta fitar, shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu yin zabe na Hukumar Festus Okoye, Ya baiyana cewa hukumar nada wa’adin kwanaki 14 domin bawa wanda ya samu nasara a kowane irin zabe takardar shaidar samun nasara.