Hukumar Zabe ta kasa mai zaman Kanta Ta sake baiyana cewa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da duk wani mutum da aka samu da lefin keta dokar zabe ta shekarar 2022 da aka yiwa gyaran fuska.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya baiyana haka a ranar Laraba a Abuja, Shugaban wanda ya samu wakilcin Shugaban Cibiyar nazari kan harkokin zabe ta kasa Farfesa Abdullahi Zuru, Yace akwai bukatar gaggauta wayar da kan jam’iyyu kan sabbin tanade-tanaden dokar zaben, da kuma tabbatar da yin aiki da ita.
Shima a nasa jawabin, Babban daraktan cibiyar, Dr Sa’ad Idris, Yace akwai bukatar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da kuma jam’iyyu suyi ganawa ta musamman kan yadda za’a inganta yin zabe a kasa, da kuma hanyoyin da za’a bi wajen dakile matsalolin dake tattare da yin zaben.