Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bukaci Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, Data jingine hukuncin da wata babbar kotun taraiyya ta yi, inda ta umarci hukumar zaben ta kasa data baiwa wadansu mutane biyu damar yin amfani da katin zabensu na wucin gadi domin yin zabe.
A kunshin karar da hukumar zaben ta shigar gaban kotun, Hukumar ta nemi kotun daukaka karar data dakatar da zartar da hukuncin da babbar kotun taraiyyar ta yi a ranar 9 ga watan Maris din bana,har sai zuwa lokacin da zata kammala sauraren karar data shigar gabanta.
Kazalika hukumar zaben ta kasa taga baiken hukuncin da babbar kotun taraiyyar ta yanke, wanda ta aiyana cewar babu inda aka yi magana kan batun katin zabe a cikin dokar zabe ta shekarar 2022, wanda ta kafa hujja da hakan a matsayin abunda zai bada damar yin zabe.
Idan ba’a manta ba, mutanen da suka kai karar hukumar zabe ta kasa a babbar kotun data yanke hukunci tun da farko,sun baiyana cewar duk da kokarin da suka rika yi na ganin sun karbi katinan zabensu na din-din din,hakan bai yuwu ba.