Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Ta yi kira ga ‘yan Najeriya dasu temakawa yunkurin hukumar na tsaftace rijistar masu yin zabe.
Kwamishinan hukumar na kasa, Festus Okoye ne yayi wannan roko a ranar Litinin, biyo bayan wasu rahotanni dake baiyana cewa, wasu kananan yara da basu kai munzali ba, na daga cikin wadanda suka yi rijistar katin zaben, gabanin babban zaben kasar nan na shekarar 2023, mai zuwa.
A yayin wata hira da aka yi dashi, ta cikin shirin Siyasa a yau, na gidan Talabijin na Channels, Y ace Hukumar ba zata iya ikirarin cewar dukkanin rijistar katin zaben da ta yi babu wani kura-kurai a cikinta ba, Ya ce a bisa haka ne ma, Sashi na 19, Ukku cikin baka na dokar hukumar, ya bata damar yin baje kolin rijistar zaben ga al’umma, domin yin gyara ko kuma shigar da wani korafi.
Ya kara da cewa, a yanzu haka ana cigaba da aikin tsaftace rijistar masu zaben, Inda ya kara da cewa wasu daga cikin jami’an hukumar na daga cikin, wadanda suka yi uwa da makarbiya wajen yiwa kanaann yaran rijista, da kuma sauran wasu matsaloli dake tattare da rijistar katin zaben na din-din din.