A karon farko a tarihi hukumar tara haraji ta tarayya ta samar da kudaden shiga Naiara trilliyan 10.1 a shekarar 2022.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, bayan ganawar shugaban hukumar da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Rahoton yace hukumar ta tara jimillar kudaden shiga na Naira trilliyan 4.09 a bangaren man fetur wanda ya kai kashi 41 da kuma Naita trilliyan 5.96 a bangaren da ba na man fetur ba wanda ya kai kashi 59 sabanin jimillar Naira trilliyan 10 da billiyan 44 da aka kudiri aniya.
Ya kara da cewa Harajin Kudaden Kamfanoni ya bayar da gudunmawar Naira tiriliyan 2.83 sai harajin kayyaki Tiriliyan 2.51 da dai sauran bangarori.