Hukumar kula da sufurin jirage sama ta kasa ta fara bincike kan dalilan da suka sa wani jirgin United Nigeriya Samfurin NUA 0506 da ya kamata ya sauka birnin Taraiyya Abuja, amma ya yi batan hanya inda ya sauka birnin Asaba na jihar Delta.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Kaftin Musa Nuhu ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Lamarin dai ya haifar da cece kuce a tsakanin jama’a musamman a kafafen sadarwar zamani.
Sai dai Hukumar ta baiwa jama’a tabbacin cewar zata yi bincike na tsanaki sannan kuma ta sake jaddada kare lafiyar masu amfani da jiragen sama a kasar nan.