Hukumar raya kogunan Hadeja Jama'are ta karyata hotanni da ake yadawa cewa dam din Tiga dake Jihar Kano ya balle.
A wata sanarwa da sakataren harkokin mulki kuma Jami'in hulda da jama'a na hukumar Salisu Baba Hamzat ya aikowa Arewa Radio, yace tun farkon watan Agusta ruwan kogin ya fara fita kuma har yanzu ruwan Yana cigaba da fita.
Sai dai yace sakamakon mamakon ruwan sama a jahohin Kaduna da Plato dam din ya kara tumbatsa kuma fitar ruwan ta karu daga kogin.
Sanarwar tace kogunan dake karkashin hukumar raya kogunan Hadeja Jama'are basu taba samun kulawa kamar a irin wannan lokaci ba musamman bayan kammala ayyukan gyara madatsun ruwa domin inganta Noman rani na TRIMMING hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar ruwa ta Najeriya da bankin duniya.
Daga nan hukumar ta Hadeja Jama'are ta bukaci masu makwaftaka da kogin su rika bada rahoton duk wani bakon abu da suka gani a dam din na Tiga yayinda hukumar ke bada tabbacin aminci da kariya daga tsarin kulawa da kogin.