Hukumar bada agajin gaggawa ta kasda NEMA a jihar Kano, ta karbi ‘yan Najeriya 13 daga birnin Khartoum na kasar Sudan a ranat talata.
Babban jami’in hukumar ta NEMA a ofishin shiyyar Kano, Dakta Nuradeen Abdullahi shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar mutanen da suka dawo Kano a ranar Talata.
Ya ce sun iso filin jirgin Mallam Aminu Kano da karfe 3 na yammaci.
Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya itace ta dawo da mutanen zuwa Najeriya a karkashin shirin kare ‘yan ci-rani hadin gwiwa da kungiyar Tarayyar Turai ga wadanda suka nuna sha’awar dawowa.
Abdullahi ya shawarci ‘yan Najeriya da su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar tafiye-tafiye da sunan neman kudi a wasu kasashe, ya kara da cewa babu wata kasa da ta fi Najeriya a garesu.