
Hukumar Hana Fasa Kwauri ta kasa reshen jihar Kaduna, Ta samu nasarar cafke wani Buhu Makare da Kakin soja wanda ake kan hanyar shigo dashi kasar nan daga Jamhuriyar Nijar, Daga tsakanin watan Maris zuwa Aprilun bana.
Shugaban hukumar reshen Kaduna, Musa Jalo wanda ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis , Ya ce jami’ansu sun kama wata mota kirar Golf Volkswagen da wani dan Najeriya ke tuka ta akan hanyar Jibia zuwa katsina.
Ya kara da cewar, Jami’ansu sun ga buhun dake cikin motar, wanda nan take suka bude shi,inda suka yi arba da kakin soji, wanda ya hada da kananan riguna da wanduna da sauransu.
Ya ce bincikensu ya gano cewar direban motar Dan asalin Najeriya ne, Kuma yana kan hanyar kai kayan ne zuwa wajen wani mutum a jihar Katsina.
Ya kara da cewar tuni aka mika buhun kayan ga hannun hukumar tsaro ta farin kaya domin zurfafa bincike, da kuma gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.