Mai rikon mukamin hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa Mista Dauda Biu, ya sha alwashin gurfanar da direbobi masu karancin shekarau da ba su da lasisin tuki a fadin Najeriya
Biu ya bayyana haka ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu ‘Danfodio da ke Sakkwato a ranar Litinin a lokacin da ya ziyarci wata daliba mai suna Fatima Suleiman ‘yar shekara 16 da wani dalibi dan shekara 18 ya kadeta a jihar yayin bikin kammala karatunsa na sakandare.
Mukaddashin wanda kwamandan hukumar na jihar Sokoto, Kabiru Nadama, ya wakilta, ya yi gargadin cewa daga yanzu duk wani direba mai karancin shekaru da aka kama yana tuki a jihar za a gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma tabbatar wa da jama'a cewa direban da aka kama zai fuskanci fushin doka.