Hukumar Kidaya ta kasa ta ce ta kashe jimillar kudi har naira milyan dubu 200 domin kimtsawa aikin kidayar mutane da gidaje ta shekarar bana, kamar yadda shugaban hukumar Nasir Kwarra ya baiyyana.
Ya fadawa manema labarai cewar kudin da aka kashe wani bangare ne na naira bilyan 800 da ake saran karba daga hannun gwamnatin taraiyya, a matsayin kasafin da ta yi domin gudanar da aikin kidayar.
Ya ce kudin an kashe su ne bayan shafe kusan shekara biyar ana tsara yadda za’agudanar da aikin kidayar.
Ya kuma baiyana cewar gudanar da aikin kidayar a zamanance abu ne mai girman gaske, kasancewar dole ne hukumar sai ta sayi Data wadda za’a yi amfani da ita wajen gudanar da aikin.