Biyo bayan korafe-korafe kan karancin samun wutar Lantarki daga al’umar jihar kano, kamfanin rarraba wutar Lantarki ta jiha KEDCO, ya Dora alhakin al’amarin akan yadda wasu ke hada wutar lantarkin ta barauniyar hanya da kuma lalata kayayyakin wutar da wasu ke yi a wasu bangarorin.
A cewar kamfanin, irin wannan matsaloli ke haifar da Gobara da jan wuta da kuma katsewar wutar a fadin jiha.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba sashen yada labarai da hulda da jama’a na kamfanin KEDCO, Ibrahim sani shawai, ya sanyawa hannu aka kuma aiko da kwapin ta nan Arewa Radio.
Daga nan kamfanin na KEDCO ya bukaci abokan Hulda dasu dauki Gabarar kare kayyakin Lantarki a yankunan su.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, a wani sako da ya fitar, shugaban kamfanin KEDCO a nan Kano, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, ya bukaci jama’a da su kasance masu alkinta kayayyakin wutar lantarki a mazaunan su, wanda hakan ne zai bada damar inganta samar da ita.
Daga nan sai ya yabawa al’umomin dake kokarin kai karar bata gari akan al’amuran satar wutar lantarki.