Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire a kasarnan JAMB ta ce za ta hukunta shugabannin jami’o’i da Magatakarda da sauran shugabannin manyan makarantu da ke ci gaba da bada gurbin karatu ba bisa ka’ida ba.
Hukumar JAMB ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Internet.
A cewar sanarwar hukumar ta JAMB ta sake nanata alwashin cewa ba za ta lamunci bada guraben karatu da wasu makarantu ke yi ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa duk ’dalibai da suka amince da duk wani gurbin karatu da aka bayar ba bisa ka'ida ba su kuka da kansu yayin da shugabannin makarantun da suka bijire wa wannan umarni zasu fuskanci hukunci daga hukumar.
JAMB ta ce zamanin da ‘dalibai ke karbar gurbin karatu ba bisa ka’ida ba, sannan kuma su matsa lamba kan hukumar ta amince da hakan ya kare domin su ma irin wadannan ‘dakibai za a daukebsu a matsayin masu laifi.