Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta kasa ICPC, ta ce ta samu nasarar karbo kadarori na kimanin Naira biliyan 2 da milyan Dari 8 a cikin shekaru uku da suka gabata ta karkashin shirin ta na bin diddigin ayyukan mazabu da kuma wanda bangaren zartarwa ke gudanarwa.
Kwamishinan Hukumar ICPC a jihar Edo, Mista Agwu Amefula, Shi ne ya bayyana haka a ranar Talata a Benin babban birnin jihar, yayin da yake jawabi a wajen wani taron wayar da kan jama’a da masu fada a ji na jihar da hukumar ta shirya.
Ya kara da cewa, hukumar ta tilastawa ‘yan kwangila 450 komawa wuraren aiyukan da aka yi watsi da su koma babu aikin domin kammala su.
Sai dai ya bukaci masu ruwa da tsaki da su sanya ido sosai kan abubuwan da suka shafi cin hanci da karbar rashawa da kuma tabbatar da gaskiya da adalci , wanda a cewarsa matsaloli ne da suka yi kaurin suna ta bangaren gudanar da aiyukan gwamnati a cikin al’umma.