Jami’an hukumar yaki da rashawa ta ICPC sun kama kimanin jami’ai 5 na sashen bada tallafi a ma’aikatar nomad a raya karkara bisa zargin karkatar da kudade.
Wata majiya ta ce binciken yana da nasaba da karkatar da kudaden da aka ware domin bibiya da kuma aiwatar da shirye-shiryen da wayar da kan jama'a.
Bayanai sunce al’amarun ya kawo cikas wajen sa ido da bibiyar tantance kayan amfanin gona.
An gano cewa an samu sama da Naira milliyan 200 a asusun bankin daya daga cikin jami’an, yayin da aka samu sama da Naira milliyan 100 a asusun bankin daya daga cikin ‘ya’yansa.
Haka kuma, an gano tsabar kudi sama da Naira milliyan 250 a gidan daya daga cikin wadanda ake zargin a Abuja.
Haka kuma binciken da jami’an ICPC suka gudanar ya nuna cewa an samu kudi sama da Naira milliyan 60 cikin watanni shida a cikin asusun bankin daya daga cikin wadanda ake zargin.
Hukumar ta ICPC ta kuma kwace kadarori da suka hada da gidan burodi da kuma asibitin gargajiya guda daya.
Da aka tuntubi kakakin hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.