Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta yi alkawarin shiryawa da kuma daukar nauyin Aurar da matasa Maza da Mata 'yan TikTok a wani mataki na kawar da rashin 'Da'a a cikin al'umma da kyautata zamantakewa.
Babban Kwamandan hukumar Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ne ya yi wannan alkawari lokacin da ya yake fadakar da 'yan TikTok da suka amsa gayyatar hukumar a ranar litinin.
Ya ce hukumar ta damu akan yadda wasu matasan Maza da Mata suka mayar da TikTok ƙafar cin mutunci da rashin tarbiya Wanda hakan ke zubar da kimar Kano.
Koda ya ke Sheik Daurawa ya yabawa wasu masu gudanar da Sana'oi da kasuwanci da masu koyar da hikimomin zamantakewa ko Ilimin Addini da na zamani a TikTok, ya ce hukumar a shirye ta ke Aurar da matasan na TikTok Maza da Mata da suke son yin Aure, Inda ya bukaci su zama jakadu na gari.