Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta bai wa kasashe damar zabar 'yan wasa 26 da za su taka leda a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.
A cikin wata sanarwa da FIFA ta fitar ta ce an kara adadin 'yan wasan da za a saka a cikin jerin 'yan wasan karshe zuwa akalla 26.
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta ce an yanke shawarar fadada 'yan wasan ne bisa la'akari da bukatar ci gaba da samun sassauci a gasar ta bana, wanda zai katse kakar wasannin kungiyoyin Turai.
UEFA ta dauki irin wannan sauye-sauye a gasar Euro a bara, bayan da masu horas da kungiyoyin turai suka bukaci hakan.