Hukumar gasa da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta tarayya ta kafa wani kwamitin bincike da zai binciki mutuwar Daraktanta na shiyyar Arewa maso Yamma, Julius Haruna.
Sakataren hukumar a Abuja, Tam Tamunokonbia, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce Haruna ya rasu ne a ofishin hukumar ranar Laraba da ta gabata a jihar Katsina.
Ya ce bayanai da aka samu sun nuna cewa Haruna ya samu sabani wanda har ya kai ga yin kaca-kaca da wata ma’aikaciyar hukumar mai suna Muibat Abdusalam.
Sakataren ya kara da cewa hukumar ta kuma ba da umarnin cikin gaggawa na dakatar da shugabancin offishin na wucin gadi da jami’an da abin ya shafa a cikin hukumar don tabbatar da bincike na gaskiya.