Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce a ranar Talata mai zuwa 6 ga watan Disambar da muke ciki ne , za ta fara aikin tantancewa tare da yin gwanjon motoci 649 da aka kwace a wasu jihohi tara na kasar nan cikinsu hadda babban birnin tarayya Abuja.
Aikin da amintattun masu gwanjon kayyakin hukumar za su yi, zai kunshi gwanjon jiragen ruwa guda 15 da hukumar ta kama a jihohin Rivers da Delta da kuma Legas sai wasu wayoyin hannu 39, Da na’urar tafi-da-gidanka 11 da sauran kayayyaki.
A sanarwar da ta fitar a jaridar The PUNCH a ranar Juma’a, ta yi cikakken bayani kan kayayyakin da za a yi gwanjon su kowace jiha, da ranakun da wuraren da za a yi gwanjon da shafukan internet da jama’a zasu iya amfani dasu domin kallon yadda gwanjon kayayyakin zai kasance.