A yau ne hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, za ta gurfanar da tsohon Babban Akanta na kasa, Ahmed Idris a gaban Kotu.
Kakakin Hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren shine ya tabbatar da haka ta wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a Abuja babban birnin taraiyya. Ya ce za a gurfanar da Idris da wasu mutane uku a gaban mai shari’a Adeyemi Ajayi na wata babbar kotun birnin tarayya Abuja.
Ya ce sauran Mutane ukun da za’a gurfanar tare da tsohon Babban Akanta na kasa bisa zarginsu da wawure tsabar kudi har Naira biliyan 109 sun hada da Godfrey Akindele da Mohammed Usman sai kuma kasuwar zamani ta Gezawa Market and Exchange Limited.
A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da kuma cin amana.
Sanarwar ta yi zargin cewa tsohon babban akanta na kasa Ahmed Idris ya kwashe kudaden ne ta hanyar amfani da wasu kwararrun kanfanonin tuntuba na bogi da kuma wasu ayyukan da ba su dace ba ta hanyar amfani da ‘yan uwansa da kuma Makusanta.
A wani bangaren kuma, Wasu Rahotanni na baiyana cewa tsohon Babban Akanta na kasa da aka dakatar, Ahmed Idris, Ya karbi cin hancin Naira biliyan 15, domin a hanzarta bin diddigin kaso 13 bisa 100 na kudaden albarkatun man fetir da ake bawa jihohin da ke hako mai a kasar nan.
A bisa tsari ana bawa jihohin kaso 13 bisa 100 na kudaden da ake samu daga bangaren man da ake hakowa a jihohin.
A cewar EFCC, Idris ya karbi kudin daga hannun Olusegun Akindele, domin ganin anyi gaggawar bawa jihohin kudin
Akindele ya kasance mataimaki na musamman ga babban Akantan tsakanin watan Fabrairu zuwa Nuwambar 2021.