Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Ai’sha Salihu Malkohi da kuma mai gidanta mai suna Abubakar Mahmoud, wanda a yanzu haka cika wandosa da iska, a gaban mai shari’a Aisha Mahmud ta babbar kotun jihar Kano, Bisa zarginsu da damfarar wata mata mai suna Farida Ibrahim tsabar kudi naira milyan 410 da dubu 518.
Hukumar ta baiyana haka ne a shafinta na X wanda aka fi sani d twitter.
Sanarwar ta ce an kama Matar ne biyo bayan korafin da wasu mutane biyu Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar gabanta, bisa zargin ma’auratan da yaudararsu, da sunan cewar zasu kawo masu motoci da wasu kayayyaki daga kasar Saudiyya.
To sai dai kuma matar ta musanta tuhumar da aka karanta mata, wanda hakan ya sa alkaliya ta dage zaman zuwa ranar 15 ga watan da muke ciki, domin sauraren bukatar bada ita beli.