Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi gargadi kan yi wadansu kalamai da basu da tushe akan kamun da ta yiwa mai sasantawa da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Kaduna, Malam Tukur Mamu.
Kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, shine ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce gargadin ya zama wajibi biyo bayan kalaman batanci da wasu jama’a suka yi kan batutuwan da suka shafi kamun da aka yiwa Tukur Mamu da kuma bincikensa da Hukumar ke yi.
Ya ce hukumar na fatan a kyale ta ta gudanar da binciken da take yi cikin tsanaki , wanda binciken shine zai faiyace inda aka dosa.
Idan ba’a manta ba, jami’an yansandan kasa da kasa sun kama Tukur Mamu ranar Talata a birnin Alkahira na kasar Masar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
Kazalika a ranar Larabar da ta gabata ne aka dawo dashi Najeriya inda kuma aka damka shi hannun jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS.