On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar Birnin Tarayya Abuja Ta yi Barazanar Matakin Shari'a Akan Masu Kasuwancin Dabbobi Barkatai Birnin Lokutan Babbar Sallah

Kwanaki tara gabanin fara bukukuwan babbar Sallah, hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja ta gargadi masu sayar da raguna da ke kokarin cin kasuwar kakar bana da su kaucewa mamaye wuraren da ba a kebe don sayar da dabbobi ba.

Babban mataimaki na musamman ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Ikharo Attah,  shine ya yi wannan gargadin a ranar Alhamis yayin da yake duba wuraren sayar da dabbobi da aka ware a yankin. 

Attah ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana sayar da raguna a wuraren da ba a amince da shi ba  za a gurfanar da shi a gaban kotu. 

Ya shawarci masu siyar da raguna  da su tuntubi hukumar kare muhalli ta Abuja domin neman yadda za su gudanar da harkokinsu ba tare da saba wa doka ba. 

A cewarsa, hukumar za ta tunkari Kotu ta kuma nemi ya ba su umarnin kwace Dabbobin, sannan  za a kai ragon gidan marayu da gidajen marasa galihu da gidan gyaran hali. 

''Tun shekara uku baya wannan ne Matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, kuma a bana ma matakin yafi tsanani. 

“Ministan ya ce babu laifi a kawo rago domin sayarwa a Abuja a yayin wannan biki na babbar sallah da  ake yi a  duniya.

“Amma abin da ministan ya ga bai dace ba, kuma ya ci gaba da gaya wa kowannenmu shi ne, kada mu bari ana sayar da raguna a wuraren da aka kebe musamman a cikin gari. "Sai dai a wurin da aka riga aka keɓe don irin waɗannan buƙatun kamar mahaukata, kasuwar raguna  a Dei-Dei, Kasuwar Kugbo da wasu ƙananan kasuwannin raguna.

 "Amma a wajen wuraren da aka kebe ba za a ba da izinin hukuma ba," in ji Attah. Ya bayyana cewa Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) karkashin jagorancin Osi Braimah, ta kafa wani kwamiti wanda ya dade yana aiki. 

Ya bayyana cewa an sake karfafa kwamatin ne domin duba yadda ake sayar da raguna, sannan ya gargadi mutane da kada su siyar da rago a wuraren da ba a kebe ba.