On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa Ta Sanar Da Naira Milyan 8 Da Doriya A Matsayin Kudin Aikin Hajjin Bana

MASALLACIN HARAMI DAKE MAKKA

Hukumar aikin hajji ta kasa ta sanar da kudin aikin hajjin bana, inda maniyyata aikin hajji da suka fito daga jihohin kudancin kasar nan zasu biya naira milyan 8 da dubu dari 8, a yayin da wadanda suka fito daga shiyyar Borno da Adamawa zasu biya naira milyan 8 da dubu dari 3.

Shugaban hukumar aikin hajji ta kasa, farfesa Abdullahi Usman ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa, ,ai dauke dasa hannun daraktar yada labaran hukumar, Fatima Sanda Usara, wadda aka fitar a Abuja.

Farfesa  Abdullahi Usman, ya ce sauran maniyyata aikin hajjin bana da suka fito daga ragowar  jihohin arewa zasu biya naira milyan 8 da dubu dari 4 a matsayin kudin aikin hajjin bana.

Shugaban y ace  an sanar da kudin aikin hajjin ne bayan  kammala  tattaunawa ta tsanaki tare da daukacin masu ruwa da tsaki.