Hukumar Hisba ta jihar kano ta yi barazanar daukar hukunci mai tsauri akan duk wani Mai tuka babur din adaidaita sahu, wanda aka samu da lika wasu hotunan batsa a jikin babur din,Ko kuma kure sautin kida a lokacin da ake tafiya.
Babban kwamandan hukumar, Sheik Harun ibn Sina, ya ce da dama daga cikin masu tuka babur din na yin shiga ta rashin da’a,wanda yin hakan ya sabawa koyarwar addinin musulunci.
A wani taron manema Labarai da hukumar ta shirya a jiya, Ya ce jami’an hukumar zasu kara saka ido kan masu aikata irin wadannan lefuka, kuma za’a hukunta su.
Dagan an sai yayi kira a gare su das u dena yin wasu abubuwa da basu dace ba, wadanda suka ci karo da koyarwar addinin musulunci.