Mukaddashin Manajan Darakta na sabon Kamfanin Jiragen sama na Najeriya, Kaftin Dapo Olumide, yace jirgin da ya yi batan dabo dauke da tambarin jirgin Najeriya Air Airline an yi hayarsa ne daga Kamfanin Jiragen Sama na Habasha domin kaddamar da tambarin.
Bayan da jirgin Boeing 737-800 ya sauka a ranar 26 ga watan Mayu da ya gabata, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana jin dadinsa da cewa kamfanin jirgin ya fara aiki bayan dogon lokaci da aka dauka da wahalhalu.
Sai dai a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sufurin jiragen sama a ranar Talata, Olumide ya ce har yanzu kamfanin na Nigeria Air bai samu lasisin gudanar da cikakken aikin sufurin jirgi ba kuma har yanzu yana kan matakin farko.
Ya bayyana cewa tun a shekarar 2018 ‘yan Najeriya suka ga tambarin da aka bayyana amma ba ainihin jirgin ba, kuma ana tunanin lokaci ya yi da za’a nuna yadda jirgin na gaske zai kasance, shi ya sa aka dauko hayar jirgin.