Kungiyar kasa da kasa da ke rajin tabbatar da cigaban fasahar sadarwar zamani wato (APC) ta nada fitacciyar mai fafutukar kare hakki kan kafofin zamani daga jihar Kano, Harira Abdulrahman Wakili, a matsayin shugaba mai kula da harkokin jinsi a Afirka.
Harira Wakili, wadda a baya ta yi aiki a matsayin jami'ar kafofin sada zumunta a cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma CITAD, tana da tarihin gwagwarmaya don kan hakokin jinsi a bangaren kafofin sadarwar zamani.
A CITAD, Wakili ta jagoranci shirye-shirye don cike gibin jinsi a fagen fasahar zamani, tare da tabbatar da kowa ya samu damar ci gaba ta yanar gizo.
A tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023, Wakili a karkashin cibiyar tallafawa cigaba kasashe ta Burtaniya, ta jagoranci shirin PLANE kan Inganta harkar Ilimi.
Shirin ya ƙarfafawa mutane da yawa da ƙwarewar da ake buƙata a fagen fasahar zamani.
Ita Jakadiya ce ta Fasahar zamani daga tushe wato Digital Grassroots, matsayin da ke nuna himmarta wajen ƙarfafawa al'umma daga tushe.
Matakin da APC ta dauka na nada Harira Wakili ya jaddada aniyarsu ta inganta cigaban jinsi a Afirka.
APC wata cibiyar sadarwa ce ta kungiyoyi da masu fafutuka, wacce aka kafa a cikin shekarar 1990, don ƙarfafawa mutane da ƙungiyoyi domin amfani da fasahar sadarwa wajen gina al'umma nufin bada gudummawar ci gaba da tabbatar da adalci da inganta zamantakewa da tsarin siyasa da dorewar muhalli.
(C)Kano Times