On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Jam'iyyar PDP Na Zargin Tinubu Da Shirya Harin Da Aka Kaiwa Ayarin Shugaba Buhari A Kano

Cikin wani yanayi na bam mamaki ko bazatta, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ce ta fara yin Allah wadai da boren da ak yiwa ayarin motocin shugaba Buhari a Kano ranar Litinin.

Wasu fusatattun matasa a Kano sun jefi tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari da duwatsu a ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya fara a jiya.

Duk da yawan jami’an tsaron da aka tsaurara, rahotanni sunce wasu fusatattun matasa dauke da duwatsu masu da sanduna daban-daban sun jefi  ayarin motocin Buhari.

An dai ga matasan da suka gudanar da zanga-zangar suna gudu domin gudun kada jami’an tsaro dauke da makamai wadanda suka bawa shugaban kasar kariya da ayarin sa suka kama su.

Idan dai za a iya tunawa a baya Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci shugaban kasar da ya dage ziyarar saboda fargabar abunda ba’a tsammanin saboda halin damuwa da ake ciki kan wa’adin da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina karbar tsofaffin takardun kudi da akasauyawa fasali.

Sai dai duk da haka gwamnan ya karbi bakuncin shugaban kasar kamar yadda akatsara tunda farko.

Har ila yau, amakon jiya ne aka yiwa  ayarin motocin shugaban kasar bore a jihar  Katsina.

Sai dai Jam’iyyar PDP ta bakin kakakinta, Hon Debo Ologunagba, ya bayyana harin a matsayin cin amanar kasa da kuma cin zarafi ga martabar Najeriya wanda kowa ya kamata ya yi Allah wadai da abunda ya faru.

Wani karin abin mamaki shi ne yadda jam’iyyar PDP ta zargi majalissar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kitsa harin domin wulakanta shugaba Buhari, a lokacin da yake ziyarar aiki a Kano.

PDP ta ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu yana nuna kyama da kuma kalamai masu kaushi ga shugaba Buhari tun bayan da shugaban kasar ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su zabi duk wani dan takara da jam’iyyar da suke so a zaben 2023.