On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Harin Bama-Bamai Kan Masu Maulidi A Kaduna Ya Fusata 'Yan Najeriya

An shiga rudani da kuma Makoki  a ranar Litinin kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar  Mutanen  kauyen 85.

Mazauna garuruwan da abin ya shafa sun ce suna gudanar da Maulidi ne, lokacin da sojoji suka jefa bama-baman, al’amarin da ya jawo Allah wadai  a cikin gida da waje.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ta ziyarci malaman addinin musulunci a jihar domin kwantar da tarzoma, yayinda  yadda gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan tashin bam din.

Kungiyar Kiristocin Najeriya da Kungiyar matasan Arewa da kungiyar kare hakki ta Human Rights Watch, da Amnesty International, da dai sauransu, sun yi Allah wadai da hare-haren bama-bamai da sojoji kaiwa.