Matatar Dangote ba ta fara samar da ganga dubu 650 a kowace rana ba bayan wucewar ranar fara aiki da Matatar a watan Agusta, wanda Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote ya sanar a baya.
Idan dai za a iya tunawa, Dangote a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen kaddamar da matatar a hukumance a watan Mayu, ya ce, samfurin farko na ayyukan matatar zai kasance a kasuwa kafin karshen watan Yuli ko farkon watan Agusta na wannan shekara.
Duk da haka, babu wani digo na mai da aka tace daga matatar man da ya shiga kasuwa makonni bayan cikar wa'adin.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta maida hankali wajen kammala matatun mai mallakinta domin Dangote dan kasuwa ne mai zaman kansa kuma zai iya yanke hukunci gobe cewa ba zai tace man ba.
Ya ce duk da cewa gwamnati na da kashi 20 cikin 100 na hannun jari a matatar, amma zaifi dacewa mu gyara namu matatun.