Dan Takarar Kujerar Sanatan Yobe Ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Bashir Machina, Ya baiyana cewa, akwai wani yunkuri da ake yi na kwaikwayar sa hannunsa a cikin wata wasika, da nufin cewar shine ya janye daga takarar.
A cewar kwamitin yakin neman zabensa, Wasu kusoshi a cikin jam’iyyar wadanda suka zama bayin cin hanci da aikata lefuka na yunkurin murde takarar kujerar sanata ta yankin.
Wata sanarwa da kakakin Yakin Neman Zabensa, Husaini Isah, Yace matakan da ake shirin dauka wata ‘kofa ce bawa Sanata Ahmad Lawan damar darewa kan kujerar.
Daga karshe Bashir Machina ya jaddada matsayarsa na cewar ba zai janye daga takarar ba, sannan kuma duk wata wasika da aka gani mai ikirarin cewa ya janye daga takarar, ba daga wajensa ta fito ba.