
'Dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP Nasiru Koguna yace har yanzun shine dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar a Kano ba Sha’aban sharaba ba.
Cikin wata wasika daya aikewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Koguna ta bakin Lauyansa Farfesa Nasiru Aliyu yace wakilan jam’iyya ne suka zabe shi amatsayin Dan takarar jam’iyyar ADP
Kazalika ya kara da cewa shi da kansa bai rubutawa hukumar zabe wasika kan janyewarsa ba, kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada .
Wasikar ta kara bayyana yadda shugaban jam’iyyar na kasa ya kirkiro da sauya sunansa ba tare da bin ka’ida ba ,kamar yadda doka ta tanada.