Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tace dokar hana amfani da babura masu kafa uku daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe har yanzu tana nan daram yayinda aka umarci jami’an rundunar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa su kama masu laifi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, an hana hawan doki da aka fi sani da Kilisa da kuma amfani da abubuwa masu tartsatsin wuta da akafisani da Knock-out, kuma za a kama wadanda suka karya doka tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Jihar Kano kasancewar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasarnan, kuma ana sa ran za’a samun masu ziyara daga ciki da wajen kasar nan, musamman a shirye-shiryen bikin Sallar Idi wanda rundunar ta ce ta sake fasalin tafiyar tsaro.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Mamman Dauda ya shawarci mutanen da ke halartar Masallatai da wuraren Tafsiri a cikin Watan mai alfarma da su kara taka tsan-tsan tare da kai rahoto ga rundunar.
CP Mamman Dauda, ya taya al’ummar Musulmi murnar sake ganin wata mai alfarma na Ramadan, domin an yi shirin samar da tsaro da nufin ganin an gudanar da azumin watan Ramadan cikin nasara da kuma bayansa.