Iyalan masarautar kasar Ingila za su yi zaman makoki na kwanaki 7, wanda zai kare bayan binne sarauniya Elizabeth, tare da kuma yin kasa-kasa da tutocin dake gidan sarautar.
A yaune Fadar mulki ta Buckingham ta bayyana cewa, za'a harba bindiga da misalin karfe 1 na rana a filin Hyde Park, inda za'a harba bindigogi 96 wanda ya kama daidai da adadin shekarun data yi a duiya
Masarautar dai bata sanar da lokacin binne gawar ba, sai dai ana tsinkayen nan da kwanaki 11 za a yi mata janaza.
Marigayiya Elizebeth ta Biyu, ta rasu tana da shekaru 96 a duniya.
Fadar tace za'a sauke tutoci zuwa kasa-kasa a gidan sarautar kasar, har zuwa bayan janazar tata, kana kuma zuwa lokacin makoki fadar zata kasance a rufe.