Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, Yace babu wani shiri da yake kan yi a halin yanzu domin yin murabus daga kan shugabancin jam’iyyar.
Da yake jawabi ta cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Simon Imobo Tsawana ya fitar a ranar Litinin, Sanata Ayu , Yace sashi na 45 da 47 da kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP yayi bayani dalla-dallla kan matakan da ake bin wajen saukewa ko kuma yin murabus daga kan shugabancin jam’iyyar PDP na kasa.
Kazalika ya kara da cewa wasu daga cikin labarai da aka kirkira dake baiyana cewa ya mika takardar murabus daga kan shugabancin jam’iyyar, ga tsohon shugaban Majalisar dattawa David Mark, Labarai ne kawai na kanzon kurege, inda ya bukaci al’umma da yi watsi dashi.
Shugaban jam’iyyar PDPn na kasa ya kara da cewa, Da yayi murabus to da zai mika takardar saukarsa daga kan kujerar ne ga mataimakinsa mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya, ba tsohon shugaban majalisar dattawa ba.